logo

HAUSA

MDD ta bayyana damuwa game da halin da shugaban jamhuriyar Nijar da ake tsare da shi yake ciki

2023-08-11 11:10:36 CMG Hausa

Babban magatakardan MDD Antonio Guterres, ya bayyana damuwa game da halin da shugaban jamhuriyar Nijar da sojoji ke tsare da shi yake ciki, yana mai cewa, shugaba Mohamed Bazoum na tsare cikin mummunan yanayi, shi da karin wasu jami’an gwamnatinsa da sojojin juyin mulkin suka cafke.

A madadin babban sakataren MDDr, mataimakin kakakinsa Farhan Haq, ya ce jami’an tsaron fadar shugaban kasar ta Nijar sun tsare Mohamed Bazoum da iyalansa, ba tare da samar musu da ruwan sha, abinci, magunguna ko lantarki ba.

Haq ya kara da cewa, mista Guterres, ya jaddada damuwarsa game da yanayin lafiya, da tsaron Bazoum da iyalansa, ya kuma sake yin kira da a gaggauta sakinsa, tare da mayar da shi kan kujerarsa ba tare da wani sharadi ba.

Har ila yau, Guterres ya ja hankali game da ci gaba da cafke karin mambobin gwamnatin shugaba Bazoum, yana mai kira da a saki jami’an ba tare da bata lokaci ba, a kuma kare hakkokin bil adama na al’ummar Nijar karkashin dokokin kasa da kasa. (Saminu Alhassan)