logo

HAUSA

An nada sabbin mambobin gwamnati a kasar Nijar

2023-08-10 14:40:15 CMG Hausa

A ranar 9 ga watan Augustan shekarar 2023 da dare aka bayyana sabbin mambobin gwamnatin rikon kwarya a kasar Nijar ta hanyar kafofin gwamnati tare da sakatare-janar na gwamnati Mahamane Roufai Laouali, wanda ya koma birnin Yamai daga kasar Chadi a wannan rana.

Daga birnin Yamai, mun tuntubi wakilinmu kai tsaye game da sabuwar gwamnati da aka kafa, Mamane Ada ko za ka ba mu karin haske game da wannan sabuwar gwamnatin?

A dunkule dai sabuwar gwamnatin na kunshe da mambobi 21 tsakanin sojoji da fararen hula. Akwai soji 6 da fararen hula 15, daga cikinsu mata 4.

Sabanin abin da ake gani, kujerar ministan kudi, shi da kansa faraminista Ali Lamine Zeine ke rike da ita.

Idan kuma aka duba ministan tsaro soji ne janar Salifou Mody. Ministan cikin gida janar Mohamed Toumba, yayin da ministan harkokin waje yake ga farar hula Bakari Yaou Sangare. Ministan kiwon lafiya manjo-kanal Garba Hakimi. ministan wasannin motsa jiki kanal Abdrouhamane Amadou. Ministan noma da kiwo, farar hula Mahaman Alhaji Ousmane. Ministan ilimi mai zurfi forfesa Mahamadou Saidou. Ministan man fetur da ma’adinai Mahamane Moustapha Barke. Ministan shari’a Alio Daouda. Ministan ilimin kasa madam Elizabeth Cherif. Ministan sufuri kanal Salissou Mahamane Salissou. Ministan ruwa kanal Maizama Abdoulaye. Ministan ma’aikata madam Aissatou Abdoulaye Tondi. Ministar tsara birane madam Aissa Lawan Wandarma, yayin da kuma wato ministar ayyukan hannu da yawon bude ido madam Guichen Agaichata Atta, sannan ministan sadarwa Sidi Mohamed Raliou. Ministan kasuwanci Seydou Asman. Sannan akwai kananan ministoci 2. Abin da dai wato ’yan Nijar suke fata wannan sabuwar gwamnati ta yi aiki, ta yadda wato kasar Nijar za ta kasance a sahon gaba a cikin nahiyar Afirka.

Mamane Ada, sashen Hausa na CRI daga Yamai a jamhuriyar Nijar.