logo

HAUSA

Sabon faraministan Nijar ya isa birnin Yamai tare samun babban tarbo

2023-08-10 10:41:20 CMG Hausa

  

Sabon faraministan kasar Nijar, Ali Mahamane Lamine Zeine a cikin jirgin saman da ya dauko shi daga kasar Chadi ya isa birnin Yamai a ranar jiya da yamma, 9 ga watan da muke ciki,  tare da samun babban tarbo daga kwamitin soja na CNSP da kuma ’yan Nijar da dama.

Daga birnin Yamai, wakilinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto: 

Da misalin karfe biyar da rabi na yamma ne, jirgin saman da ke dauke da sabon faraministan kasar Nijar Ali Lamine Zeine da shugaban kwamitin soja na CNSP janar Abdrouhamane Tchiani ya nada a ranar 7 ga watan Augustan shekarar 2023, ya sauka a filin jiragen saman kasa da kasa na Diori Hamani da ke birnin Yamai. Daga saukarsa daga jirgin saman da hukumomin kasar Chadi suka kebe domin kawo shi a birnin Yamai, Ali Mahamane Lamine Zeine ya samu tarbo daga mambobin kwamitin soja na CNSP da kuma sakatarorin ma’aikatun gwamnati da mambobin iyalinsa dake birnin Yamai. Shi da sabon faraministan Nijar ya amince da wannan mukami da zummar kawo tashi gudunmawa ga ci gaban tattalin arzikin Nijar da na al’umma tun bayan juyin mulkin ranar 26 ga watan Yulin shekarar 2023 da ya sauke mulkin jamhuriya ta bakwai a karkashin jagorancin tsohon shugaban kasa Mohamed Bazoum.

’Yan Nijar da dama ne suke ganin nada Ali Lamine Zeine a kan wannan kujera, abin alfahari ne ga makomar kasar Nijar, ganin cewa kwararre ne a fannin tattalin arziki da siyasar kasa da kasa, haka zalika nadin nasa ya samu karbuwa daga dukkan bangarorin al’ummar Nijar bisa ga cewa mutum ne mai dattako da kishin kasa, da kuma ya nuna iyar aikinsa a lokacin da ya rike mukamin ministan kudi a zamanin mulkin Tandja Mamadou.

Tun daga zauren baki dake filin jiragen saman Diori Hamani ne, jama’a suka nuna masa tarbo har zuwa masaukinsa, cikin kide-kide da bushe-bushe cikin ayarin motoci da babura da kuma mazauna birnin Yamai da suka fito kan hanya domin yi masa maraba da zuwa.

Jim kadan bayan zuwa nasa faraminista Ali Lamine Zeine ya isa fadar shugaban kasa dake birnin Yamai inda ya gana da shugaban kasa, shugaban kwamitin soja na CNSP janar Abdrouhamane Tchiani.

Mamane Ada, sashen hausa na CRI daga Yamai a jamhuriyar Nijar.