logo

HAUSA

Taron ministocin kula da ayyukan gona na kasashen BRICS na mayar da hankali kan wadatar abinci

2023-08-10 10:44:53 CMG Hausa

Damuwar da ake da ita game da wadatar abinci da mummunan tasirin rikicin yankuna kan tsarin samar da abinci da amfanin gona, ya zama muhimmin batu a taron ministocin kula da ayyukan gona na kasashen BRICS, wanda ke gudana a lardin Limpopo na kasar Afrika ta Kudu.

Darakta janar na hukumar raya ayyukan gona da kula da filaye da raya karkara na kasar Afrika ta Kudu Mooketsa Ramasodi, ya shaidawa manema labarai a jiya cewa, taron zai samar da wani tsari da zai kasance cikin tsare-tsaren ayyukan BRICS tsakanin shekarar 2021 zuwa 2024.

An fara taron mai taken “Karfafa hadin gwiwa domin samun amfanin gona mai dorewa da kara yawan amfanin gona” daga ranar Talata, inda za a kammala shi a gobe Juma’a. (Fa’iza Mustapha)