logo

HAUSA

Sin ta yi kira da a shawo kan rikicin Sudan ta hanyar gudanar da shawarwari

2023-08-10 09:38:55 CMG Hausa

Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Dai Bing ya yi kira da a kawo karshen tashin hankali a Sudan. Dai Bing wanda ya yi kiran yayin zaman kwamitin tsaron MDD na jiya Laraba, ya ce rikicin kasar Sudan ya doshi watanni 4, lamarin dake kara haifar da asarar rayukan fararen hula, da kara tabarbarewar yanayin jin kai.

Jami’in ya kara da cewa, a matsayin Sudan na kawa, kuma abokiyar huldar kasar Sin, kasar Sin din tana matukar damuwa da halin da ake ciki a Sudan, kuma Sin na fatan dukkanin sassan da rikicin kasar ya shafa za su sanya moriyar kasa, da al’ummar ta gaban komai, kana za su goyi bayan matakan dakile kara tabarbarewar al’amura, su kuma warware rikicin dake wakana ta hanyar tattaunawa, ta yadda za a samar da yanayin dawo da zaman lafiya da sasanto. (Saminu Alhassan)