logo

HAUSA

Fasahar aikin gona da ire-iren hatsi masu inganci na Sin a bikin baje kolin Uganda

2023-08-10 20:39:34 CMG HAUSA

 

Kwanan baya, an gudanar da bikin baje kolin aikin noma karo na 29 na kasar Uganda a birnin Jinja dake gabashin kasar, masanan shirin hadin kan kasashe masu tasowa na Sin da kungiyar hatsi ta MDD wato FAO da Uganda, sun kawowa bikin wasu sabbin fasahohin aikin gona da ire-iren hatsi masu inganci, abubuwan dake samun karbuwa matuka.

An gudanar da wannan biki daga ran 4 zuwa 12 ga watan, wanda ya hallara tawagogi fiye da 250.

Mai jagorancin tawagar masanan Sin Zhang Xiaoqiang ya bayyana cewa, manoma a wurin sun kara fahimtar fasahohin aikin gona na kasar Sin a bikin, ta yadda karin manoma za su amfana da wadannan sabbin fasahohi da ire-iren hatsi. Matakin da zai kara yawan hatsi da za a samar, da ma ingiza kudin shigar manoma da dai sauransu. (Amina Xu)