logo

HAUSA

Ana kokarin yin amfani da tauraron dan Adam wajen dakile kamfar abinci a Afirka

2023-08-09 13:53:15 CMG Hausa

An bude taron masana daga kasashen nahiyar Afirka, game da amfani da tauraron dan Adam wajen tattara bayanai da ka iya taimakawa wajen dakile kamfar abinci a Afirka.

Yayin taron na yini 3 da aka bude jiya Talata a birnin Nairobin kasar Kenya, karkashin jagorancin cibiyar shiyya ta 7, ta tattara alkaluman albarkatu domin samar da ci gaba ko RCMRD, mahalartan da yawansu ya haura 1,000, ciki har da manyan jami’an gwamnatoci, da masana kimiyya daga kasashen Afirka 20, da ma wasu wakilai daga kungiyar AU da MDD, sun nazarci dabarun sanya ido kan yanayin doron kasa, don karfafa ikon shiyyar a fannin raya aikin gona.

A jawabinsa na bude taron, babban jami’in kimiyya a hukumar gudanarwar kungiyar AU Mahaman Bachir Saley ya ce, irin hotunan doron kasa da tauraron dan Adam ke dauka daga sama, na iya taimakawa gwamnatocin kasashen Afirka, wajen sanya ido kan amfanin gona dake sassa daban daban.  (Saminu Alhassan)