logo

HAUSA

Burundi Da Sin Sun Kulla Yarjejeniyar Zamanintar Da Babban Filin Jirgin Saman Burundin

2022-02-27 16:41:44 CRI

A ranar Asabar, kasashen Burundi da Sin sun sanya hannu kan yarjejeniyar aikin fadadawa da zamanintar da filin jirgin saman kasa da kasa na Melchior Ndadaye, dake Bujumbura, babban birnin kasar Burundi.

An gudanar da bikin sanya hannu kan yarjejeniyar ne a ma’aikatar harkokin wajen Burundi, wanda ministan harkokin waje da bunkasa hadin gwiwa na kasar Burundi, Albert Shingiro, da jakadiyar kasar Sin a kasar Burundi, Zhao Jiangping suka jagoranta.

Zhao ta ce, aikin ya hada da bangarori uku, wato gyaran titinan jirgin sama, da wajen taruwar jiragen, da gina cibiyar sadarwa domin kula da tashi da saukar jirage, da ginin tafiyar da harkoki, da kuma samar da kayayyaki a fannonin ayyukan kula da sufurin jiragen sama, aikin sadarwa da hasashen yanayi.

Jakadiyar ta kara da cewa, wannan aiki ya kara bayyana ingantacciyar huldar ‘yan uwantaka dake tsakanin kasashen Sin da Burundi. Ta ce abokantakar dake tsakanin kasashen 2 ta kasance ta amincewar juna ce, da nuna wa juna goyon baya, da kuma samun moriyar juna.

A nasa bangaren, ministan harkokin wajen Burundin Shingiro ya ce, wannan wani muhimmin aiki ne da zai kara kyautata huldar dake tsakanin kasashen biyu.(Ahmad)

Ahmad