Samun ciki yana taimaka wajen rage barazanar kamuwa da ciwon sankarar mahaifa
2021-11-08 16:33:17 CRI
Wani sabon nazari da masu nazari na kasar Australiya suka gudanar ya gano cewa, samun ciki yana taimakawa wajen rage barazanar kamuwa da ciwon sankarar mahaifa wato endometrial cancer. Idan mata suka kara samun ciki sau da dama, to, barazanar da za su fuskanta tana kara raguwa. Ko da sun zub da ciki, ba su haihu a karshe ba, samun cikin yana iya kare su daga kamuwa da ciwon sankarar.
Masu nazari daga kwalejin ilmin likitanci na Berghofer na kasar Australiya sun yi nuni da cewa, sun tantance bayanan samun ciki daga nazarce-nazarce guda 30 na kasa da kasa, wadanda suka shafi mata kusan dubu 17 masu fama da ciwon sankarar mahaifa wato endometrial cancer da kuma mata kusan dubu 40 wadanda ba su taba kamuwa da ciwon ba.
Masu nazarin sun yi bayani da cewa, alkaluman kididdigar sun shaida cewa, idan an cika watanni 40 da samun ciki sa’an nan an haihu sau daya, to, barazanar kamuwa da ciwon sankarar mahaifa wato endometrial cancer ta ragu da kaso 15 cikin dari. Idan an zub da ciki ba a haihu a karshe ba, to, barazanar kamuwa da ciwon sankarar mahaifa wato endometrial cancer ta ragu da kaso 7 cikin dari. Amma haihuwar tagwaye ko haihuwar jarirai da dama a karo guda ba zai taimaka wajen kara rage barazanar kamuwa da ciwon sankarar mahaifa wato endometrial cancer ba.
Dangane da nazarin, madam Zhang Chuji, wata likita ce da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta yi mana karin bayani da cewa, wannan nazari ya nuna mana cewa, a matakin ciki na karshe, wato gab da haihuwa, yawan sinadarin jikin mata na Progesterone Prog ya kan karu sosai. Kana kuma masu juna biyu suna samun wasu sauye-sauye a jikunansu a farkon lokacin samun ciki. Watakila dukkansu na taimaka musu rage barazanar kamuwa da ciwon sankarar mahaifa wato endometrial cancer. (Tasallah Yuan)
Labarai Masu Nasaba
- Haramta amfani da mai dake da guba ya ceto rayukan miliyoyin mutane da magance cututtukan jijiya
- Kila rashin kwanciyar hankali tsakanin miji da mata zai kawo illa ga dabi'ar ‘ya’yansu
- Yin rigakafin kamuwa da ciwon bakin ciki yayin da aka samu ciki
- Rayuwa ta hanyar da ta dace yana iya kare mutane daga kamuwa da ciwon karancin basira