MDD ta sanar a kwanakin baya cewa, duniya ta kawo karshen amfani da wani sinadari mai guba a cikin mai, wanda ya yi kaurin suna wajen haddasa mutuwar miliyoyin mutane da bai kamata a ce sun mutu ba.
Matatun mai a fadin duniya, sun kara sinadarin tetraethyllead a cikin bututun mai don kara aikin injuna. Gurbatacciyar iskar da ake fitarwa daga motocin da ke amfani da man, ta haddasa mutuwar wuri na mutane miliyan 1.2, inda gwamnatoci ke kashe sama da dalar Amurka tiriliyan 2.44 a duk shekara don magance matsalolin da sinadarin ke haifarwa.
Kasar Aljeriya ta kawo karshen sanya wannan mahadi cikin mai ne daga watan Yulin shekarar 2021, wanda ya sa duniya gaba daya ta tsira daga man fetur mai surki a cikinsa.
Inger Andersen, babbar daraktar zartaswa ta hukumar shirin kare muhalli na MDD (UNEP) ta ce, nasarar aiwatar da dokar hana amfani da man fetur da aka surka da guba, wata babbar nasara ce ga lafiyar al’ummar duniya da muhallin mu.
Wasu jerin sakamakon binciken sun tabbatar da cewa, gurbatacciyar iskar gas da aka fitar sakamakon amfani da man fetur da aka surka da guba ta gurbata iska, ruwa da kasa, haka kuma yana lalata sassan jiki da ‘yan tayi.
An fara amfani da sinadarin mai guba a cikin man fetur a 1922, kafin shekarar 1970, kusan dukkan matatun mai a fadin duniya sun gauraya sinadarin a cikin man fetur. Daga nan ne kuma hayaki mai guba ya fara haifar da karuwar mace-macen wuri da kuma matsalolin jijiyoyin jiki, lamarin da ya sa gwamnatocin kasashe suka fara hana amfani da sinadarin a cikin mai.
An kaddamar da wani gangami na kawo karshen amfani da man da aka gauraya sinadarin mai guba a ciki a shekarar 2002. Sai dai kuma shirin, ya kwashe fiye da shekaru 19 kafin hukumomin kiyaye muhalli su shawo kan gwamnatoci su yi amfani da wasu sinadarai na daban don maye gurbin sinadarin mai guba da aka sanya cikin man fetur.
Lalle hayaki mai guba da ake fitarwa daga iri wannan mai, ya haifar da cututtuka daban-daban na lafiya. Sai dai, UNEP da sauran kungiyoyi sun shafe kimanin shekaru 19, don tabbatar da ganin gwamnatoci sun kawo karshen sanya wannan sinadari a cikin mai.
Har yanzu ana ci gaba da yaki da harkar sufuri mai gurbata muhalli, inda hukumar UNEP ke fafutukar ganin an rage sanya sinadarin sulfur a cikin mai, da samar da injuna masu inganci da sauyawa zuwa motoci masu amfani da lantarki. A hannu guda kuma, su ma kungiyoyin kare muhalli, suna ta kokarin kawo karshen amfani da sinadarin lead a cikin fenti.