logo

HAUSA

Sin zata bunkasa amfani da makamashi mai tsafta a kauyuka da biranen kasar

2022-02-25 15:43:31 CMG

Sin zata bunkasa amfani da makamashi mai tsafta a kauyuka da biranen kasar_fororder_0225-Ahmad-muhalli-Sin

Ma’aikatar kula da gidaje ta kasar Sin, ta bayyana aniyar kasar na saukaka hanyoyin amfani da makamashin da baya gurbata muhalli a tsarin gudanar da ayyukan gine-gine a birane da yankunan karkara, a kokarin da kasar ke yi don cimma burinta na rage fitar da hayaki mai gurbata muhalli, da kuma cimma muradin kaiwa matsayin koli na shirin takaita hayaki mai gurbata muhalli.

A jawabin da ma’aikatar kula da gidaje ta kasar ta gabatarwa taron manema labaru a ranar Alhamis, mataimakin ministan ma’aikatar kula da gidaje da raya karkara da birane na kasar, Zhang Xiaohong, ya ce, za a yi dukkan kokarin da ya dace wajen inganta tsarin ayyuka a kauyuka da birane, kana za a sanya tsauraran dokoki dake shafar tsarin gudanar da dogayen gine-gine.(Ahmad)

Ahmad