logo

HAUSA

Jami’an Sin da Nijer sun tattauna batun raya aikin gine-gine

2022-02-22 15:11:05 CMG

Jami’an Sin da Nijer sun tattauna batun raya aikin gine-gine_fororder_220222-Bello-Niger

A jiya Litinin, jakadan kasar Sin a jamhuriyar Niger, Jiang Feng, da minista mai kula da ayyukan raya garuruwa da samar da gidaje na kasar Niger, Maizoumbou Amadou, sun gana da juna, inda suka tattauna batun raya huldar hadin kai tsakanin kasashen biyu, musamman a fannin raya birane da kuma gina gidajen kwana.

Jakada Jiang na kasar Sin, ya bayyana fatansa na ganin karin kamfanonin kasar Sin sun shiga a dama da su a aikin raya biranen kasar Niger. A cewarsa, kasar Sin na son karfafa hadin kai da mu’ammala tare da bangaren Niger, a fannin raya garuruwa da gina karin gidaje.

A nasa bangaren, Malam Maizoumbou Amadou ya ce, ita ma kasar Niger tana da burin karfafa hadin gwiwa tare da kasar Sin, kana kasar na son tura wasu tawagogi zuwa kasar Sin, don koyon muhimman fasahohi da Sin ta samu. (Bello Wang)

Bello