logo

HAUSA

Adadin baligai masu fama da hawan jini ya ninka cikin shekaru 30 da suka gabata

2021-11-08 16:35:06 CRI

Adadin baligai masu fama da hawan jini ya ninka cikin shekaru 30 da suka gabata_fororder_src=http___img.365azw.com_Attachments_share_201705_590801d282777!article.w.p&refer=http___img.365azw

Wani sakamakon bincike da aka gudanar a kwanan baya ya nuna cewa, adadin baligai wadanda ke fama da matsalar hawan jini, ya ninka a cikin shekaru 30 da suka gabata, inda aka fi samun galibin irin wannan matsala a cikin kasashe masu karanci da matsakaicin kudin shiga.

Abin mamaki shi ne, kusan kashi 41 na mata da kashi 51 na maza masu fama da matsalar hawan jini, ba su da masaniya game da yanayin lafiyarsu, a cewar binciken jaridar The Lancet. Sakamakon haka, sama da rabin baligai, ba sa karbar magani a shekarar 2019, wanda ya jefa su cikin hadarin kamuwa da cututtukan zuciya.

Binciken ya bayyana cewa, sama da mutane miliyan 8.5 da suka mutu a duniya, na da alaka kai tsaye da matsalar hawan jini a kowace shekara. Bugu da kari, mutanen da ke fama da wannan yanayi, suna cikin hadarin gamuwa da shanyewar gyefen jiki, da cututtukan zuciya mai tsanani da cututtukan koda.

Masu binciken sun yi nuni da cewa, rage hawan jini na iya rage matsalar shanyewar jiki da kashi 35 zuwa 40 cikin dari, bugun zuciya da kashi 20 zuwa 25 cikin dari, da tsayawar zuciya da kusan kashi 50 cikin dari.

Binciken ya nazarci bayanan hawan jini na mutane miliyan 100 daga kasashe 184 don kididdiga yawan mutanen da ke rayuwa da matsalar hawan jini.

Duk da babban hadarin da ke tattare da yanayin, kasashe masu karanci da matsakaicin kudin shiga a yankin Afirka da ke kudu da hamadar Sahara da nahiyar Oceania, Nepal da Indonesia ba su sami ci gaba sosai ba.

Kasa da kashi 1 cikin 4 na mata, da kasa da kashi 1 cikin 5 na maza masu fama da hawan jini sun sami magani don daidaita karfin bugun jininsu a shekarar 2019, kuma kasa da kashi 10 cikin 100, suna da karfin sarrafa karfin jini, in ji binciken.

Sakamakon farko da samun jiyya, sun taimaka wajen rage matsalar hawan jini tsakanin al’umma a cikin kasashe masu samun kudin shiga mai yawa. Maimaita irin wannan aikin na iya taimakawa wajen magance matsalar hawan jini a kasashe masu karanci da matsakaicin kudin shiga, da rage nauyi akan tsarin kiwon lafiya.

Masu nazarin sun yi gargadin cewa, rashin ganowa da ma yin jiyya da ke ci gaba da kasancewa a cikin kasashe mafiya talauci a duniya, gami da karuwar adadin mutanen da ke fama da hawan jini, za su canza kaso mai yawa na masu fama da cututtukan jijiyoyin jini da na koda zuwa yankin Afirka da ke kudu da hamadar Sahara, nahiyar Oceania da kudancin Asiya. Don haka inganta karfin wadannan kasashe don ganowa da ba da jinyya ga masu fama da matsalar hawan jini, wani bangare ne na matakin farko na kula da lafiya da ma lafiyar duniya baki daya.

Tasallah Yuan