logo

HAUSA

Kasar Sin na taimakawa kasashen Afirka shawo kan fari da tamowa

2022-02-24 14:16:32 CMG

Kasar Sin na taimakawa kasashen Afirka shawo kan fari da tamowa_fororder_220224-Bello-aikin noma

A baya-bayan nan, hukumar abinci ta duniya WFP ta yi gargadin cewa, yankin ‘kahon Afirka’ dake arewa maso gabashin nahiyar, na fuskantar fari mafi muni tun bayan shekarar 1981, lamarin da ya sanya mutane kimanin miliyan 13 fuskantar yunwa. Don tinkarar wannan matsala, hukumar WFP ta kaddamar da shirin kai dauki, inda ake tara kudi don samar da abinci ga mutanen dake ‘kahon Afirka’. Kuma kasar Sin ma ta shiga wannan aiki.

Sa’an nan a wajen wani taron tattauna ayyukan aiwatar da sakamakon da aka cimma a taron ministoci na 8 na dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka, da ya gudana a karshen watan Nuwambar bara, Wu Peng, darektan shashen Afirka na ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, ya yi bayani kan wasu ci gaban da aka samu, musamman ma a fannonin rage talauci da tallafawa manoma a kasashen Afirka, inda ya ce,

“Kasar Sin ta shirya a bangarorin nuna fasahohin aikin gona na zamani, da horar da manoma, inda take fatan aiwatar da hadin gwiwa mai karfi tare da kasashen Afirka. Kana kasar Sin ta saukaka wa kasashen Afirka ayyukan shigar da amfanin gona zuwa kasar, matakin da zai ba su damar inganta fitar da kayayyaki, da raya aikin gona, gami da samun karin kudin shiga.” (Bello Wang)

Bello