Ministocin Harkokin Wajen Sin Da Jamus Sun Tattauna Ta Wayar Tarho Kan Batun Yanayin Da Ake Ciki A Ukraine
2022-02-27 16:02:23 CRI
Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, a jiya Asabar, ya tattauna ta wayar tarho da ministar harkokin wajen kasar Jamus, Annalena Baerbock, inda suka yi musayar ra’ayoyi game da halin da ake ciki a kasar Ukraine.
Wang ya ce, kasar Sin tana mayar da hankali matuka game da halin da ake ciki a Ukraine, kuma tana goyon bayan duk wani kokari mafi dacewa na kashe wutar rikicin, da kuma cimma nasarar warware rikicin ta hanyoyin siyasa.
Game da batun tsaron Turai, Wang ya ce, kamata ya yi a dauki damuwar dukkan kasashe da muhimmanci, ya kara da cewa, biyo bayan zagaye biyar na aikin kara shigar da mambobi cikin kungiyar tsaron NATO a gabashin Turai, ya kamata a yi kokarin daidaita bukatun Rasha ta fannin tsaron kasa ta hanya mafi dacewa.
Ministan harkokin wajen kasar Sin ya ci gaba da cewa, yakin cacar baka ya riga ya zo karshe. Ya zama tilas kungiyar NATO ta sake la’akari da matsayarta, da hakkokin dake bisa wuyanta, ya kara da cewa, kasar Sin ya yi amanna cewa, wajibi ne a yi watsi da dukkan wani tunani na yakin cacar baka da yin fito-na-fito a kungiyance. Kasar Sin tana goyon bayan kungiyar NATO, da kungiyar tarayyar Turai, da kasar Rasha, da su koma ga teburin tattaunawar sulhu, kuma su yi kokarin gina wani tsarin tsaron Turai mai adalci, da inganci da dorewa, kuma wacce za ta tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali mai dorewa a nahiyar Turai.
Wang ya kuma bayyana cewa, kasar Sin ba ta goyon bayan warware rikicin ta hanyar sanya takunkumi, kuma tana matukar Allah wadai da matakin ra’ayin sanya takunkumi na bangare guda, wanda ya ci karo da dokokin kasa da kasa.(Ahmad)
Labarai Masu Nasaba