logo

HAUSA

Yin rigakafin kamuwa da ciwon bakin ciki yayin da aka samu ciki

2021-11-08 16:26:26 CRI

Yin rigakafin kamuwa da ciwon bakin ciki yayin da aka samu ciki_fororder_u=2590682857,1536050448&fm=26&fmt=auto

Wani nazarin da aka gudanar a jami’ar Queensland ta kasar Australiya ya nuna cewa, idan iyaye mata suka kamu da ciwon bakin ciki yayin da suka samu ciki da kuma bayan haihuwa, to, zai illata lafiyarsu da ma kawo illa ga yadda ‘ya’yansu za su girma yadda ya kamata. Don haka ya kamata a yi rigakafin kamuwa da ciwon bakin ciki tun daga lokacin samun ciki.

Kafin wannan kuma, masu nazari daga jami’ar Queensland da jami’ar Newcastle ta kasar Australiya sun gudanar da wani nazari kan lafiyar mata ‘yan kasar Australiya cikin hadin gwiwa, bisa taimakon kudi daga gwamnatin kasar, inda suka yi nazari kan lafiyar mata ‘yan Australiya fiye da dubu 57 a jiki da ma tunani da kuma batutuwan da suka shafi lafiyarsu. Nazarin da muka ambata a baya wanda jami’’ar Queensland ta gudanar an gudanar da shi ne bisa tushen bayanan da aka samu daga wadannan nazarce-nazarce 2.

Masu nazarin sun tantance bayanan lafiyar iyaye mata 892 da kuma ‘ya’yansu 978, dangane da bakin ciki da suka shiga kafin sun samu ciki, a lokacin da suka samu ciki, da bayan haihuwarsu, da kuma yadda ‘ya’yansu suka girma da kuma kwarewarsu. 

Sakamakon nazarin ya shaida cewa, idan masu juna biyu suka kara daukar tsawon lokaci suna cikin bakin ciki yayin da suka samu ciki, to, zai kara yi wa ‘ya’yansu mummunar illa.

Masu nazarin sun yi bayani da cewa, a cikin dukkan mata wadanda suka gudanar da nazarin kansu, daya daga cikin ko wadanne 5, ta taba kamuwa da ciwon bakin ciki.

To, ko akwai shawarar da za a iya bai wa mata? Madam Zhang Chuji, wata likita ce da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta gaya mana cewa, kamata ya yi a yi rigakafin kamuwa da ciwon bakin ciki tun daga lokacin samun ciki, har bayan haihuwa da ma lokacin yarantakar kananan yara. Haka kuma, wajibi ne matan da suka nuna alamar kamuwa da ciwon bakin ciki su je ganin likita kan lokaci ko kuma neman samun taimako daga kwararru da hukumomi masu ruwa da tsaki. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan