logo

HAUSA

Zelensky: Ukraine a shirye take ta tattauna da Rasha amma ba a kasar Belarus ba

2022-02-27 20:50:14 CRI

Shugaban kasar Ukraine, Volodymyr Zelensky ya yi watsi da bukatar da Rasha ta gabatar game da shiga tattaunawar sulhu a kasar Belarus, inda ya gabatar da wasu biranen da yake ganin dacewar tattaunawar, da suka hada da Budapest da Warsaw.

Zelensky ya yi wannan tsokaci ne a jawabin da ya gabatar ta kafar bidiyo, wanda aka wallafa ta shafinsa na Telegram a yau Lahadi, jim kadan bayan fadar Kremlin ta sanar cewa, wakilan kasar Rasha sun isa kasar Belarus, kuma sun shirya fara tattaunawar da kasar Ukraine a birnin Gomel.

Zelensky yace, Ukraine a shirye take ta tattauna da Rasha, amma ba a kasar Belarus ba, saboda Rasha ta kaddamar da wasu daga cikin hare-harenta daga kasar Belarus.

Ya ce, “muna son zaman lafiya, muna son tattaunawa, muna son kawo karshen yaki, duk wani birnin da za a gabatar mana mun amince da shi, a kowace kasa yake, wadda ba a yi amfani da wani yakinta wajen kaddamar da hare-haren makami mai linzami kanmu ba." Zelensky ya kara da cewa, Ukraine ta gabatar da bukatar yin tattaunawar a wasu sauran kasashe kamar Poland, Hungary, Turkey da Azerbaijan, amma ya zuwa yanzu Rasha ta ki amincewa. (Ahmad)

Ahmad