logo

HAUSA

An sanar da dokar ta-baci a Ukraine

2022-02-24 14:13:29 CMG

An sanar da dokar ta-baci a Ukraine_fororder_220224-Bello-Ukraine

Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky, ya zartas da dokar ta-baci mai wa’adin kwanaki 30 a daukacin yankunan kasar, ban da jihohin Donetsk da Luhansk, dokar ta fara aiki ne daga yau, 24 ga wata.

Dokar ta-bacin ta hana gudanar da gangami, da zanga-zanga, da yajin aiki, da sauran ayyukan da za su haddasa taruwar jama’a. Kana an haramtawa sojoji sauya wuraren zamansu, da tsaurara manufar da ta shafi shigi da fici. An ce za a iya daukar matakan hana fita da dare, da takaita zirga-zirga, idan akwai bukata.

A nashi bangaren, Alexey Danilov, sakataren kwamitin tsaron kasar Ukraine, ya ce kasar Rasha ta gabatar da wasu dokoki masu alaka da yankunan kasar Ukraine, wadanda “ba su da amfani”, sa’an nan dole ne kasar Ukraine ta mayar da martani kan matakan da kasar Rasha ta dauka. (Bello Wang)

Bello