logo

HAUSA

Kasar Sin Ta Kammala Aikin Ba Da Taimakon Abinci A Kenya

2022-02-15 13:52:22 CRI

Kasar Sin Ta Kammala Aikin Ba Da Taimakon Abinci A Kenya_fororder_kenya

Gwamnatin kasar Kenya da ofishin jakadancin kasar Sin a kasar, sun sa hannu kan takardar shaidar mika abincin da yawansa ya kai ton 11835, wanda darajarsa ta kai dalar Amurka miliyan 12 jiya Litinin a birnin Nairobi. Wannan ya shaida cewa, an cimma nasarar kammala aikin ba Kenya taimakon abinci cikin gaggawa.

A shekarar 2018 ne gwamnatin Sin ta sa hannu kan takardar aikin, inda ta bai wa Kenya abinci a rukunoni 8.

An dauki shekaru da dama ana fama da fari a kasar ta Kenya. A watan Satumban shekarar 2021 ne shugaban Kenya ya sanar da ayyana fari a matsayin bala’in da ya shafi kasar baki daya. A ranar 8 ga wata kuma, hukumar tsara shiri kan abinci ta duniya karkashin inuwar MDD ta bayyana cewa, wasu kasashe da ke yankin kahon Afirka suna fama da tsananin fari, wanda ba a taba ganin irinsa ba cikin shekaru fiye da 40 da suka wuce, inda mutane miliyan 13 suke fama da mummunar matsalar karancin abinci a kasashen Habasha, Kenya, da Somaliya. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan