logo

HAUSA

Kenya za ta inganta fitar da fina-finai zuwa ketare

2021-10-23 16:12:52 CRI

Kasar Kenya ta shirya inganta fitar da fina-finai zuwa kasashen waje domin bunkasa samun kudin shiga daga kasashen ketare.

Shugaban hukumar kula da fina-finai ta kasar Kenya wato KFC Timothy Owase, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a birnin Nairobi, hedkwatar kasar Kenya jiya Jumma’a cewa, kasar za ta dogara kan hada hannu da abokan huldarta na kasashen ketare, wajen shirya fina-finai domin tabbatar da sun samu karbuwa daga masu kallo na kasashen waje.

Jami’in ya kara da cewa, za a fadada kasuwar fina-finan kasar Kenya, ta hanyar nuna su a bukukuwan fina-finai na kasashen waje.

A cewar hukumar KFC, kasar Kenya tana da sahihan labaran da za su samu karbuwa a wajen sauran kasashen Afrika, har ma da sauran kasashe na sassan duniya.

Shugaban ya ci gaba da cewa, ta hanyar inganta talla, fina-finan Kenya na da damar samun karbuwa a duniya.

Har ila yau, ya ce Kenya za ta ba da fifiko ga fitar da fina-finanta zuwa kasashen ketare, domin za su kara bayyana kyawawan al’adun gargajiya na kasar ga al’ummun kasashen waje. (Fa’iza Mustapha)

Fa’iza Mustapha