logo

HAUSA

Hadin gwiwar Sin da Afirka na goyon bayan yadda Afirka ke sauyawa ga makamashi maras gurbata muhalli

2021-11-26 10:04:31 CMG

Hadin gwiwar Sin da Afirka na goyon bayan yadda Afirka ke sauyawa ga makamashi maras gurbata muhalli_fororder_211126-Kenya-SA

Alkaluma na hukuma sun nuna cewa, karfin makamashin wutar lantarki bisa karfin hasken rana da aka girka a kasar Kenya, ya haura megawatt 100, yayin da irin wannan makamashi da kasar Sin ta dauki nauyin samar da shi a tashar Garissa ta kasar Kenya, ya kai megawatt 50.

A cewar shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta, tashar samar da wutar lantarki ta hasken rana dake Garissa, ta dora kasar Kenya kan turbar samun isasshen makamashi mai kiyaye muhalli, da kara daga martabar Kenya a matsayin cibiyar samar da makamashin da ba ya illa ga muhalli a Afirka. Shugaba Kenyatta ya ce, yana daga cikin dabarun gwamnatinsa na sabunta makamashin da ake iya sabuntawa, wajen samar da girbi megawatt 400 na wutar lantarki daga dimbin albarkatun hasken rana da Allah ya horewa kasar.

Masanin hulda da kasa da kasa mazaunin Kenya Cavince Adhere, ya rubuta a cikin sharhin da ya rubuta a farkon wannan wata cewa, kasar Sin ita ce abokiyar hadin gwiwa dake kan gaba a kudirin nahiyar, ta sauyawa ga salon makamashin da ake samu daga hasken rana da kuma iska.

Adhere ya ce, taron ministoci karo na takwas na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka (FOCAC) da za a yi a birnin Dakar na kasar Senegal, ya samar da wani dandali na lalubo hanyoyin kirkire-kirkire, inda abokan hulda na dogon lokaci za su kara karfafa yaki da sauyin yanayi.(Ibrahim)

Ibrahim