logo

HAUSA

Gudummawar Riga-kafin Da Sin Ta Samar Sun Isa Kenya

2021-09-19 16:51:17 CRI

Gudummawar Riga-kafin Da Sin Ta Samar Sun Isa Kenya_fororder_kenya

Manyan jami’an gwamnatin kasar Kenya sun karbi gudummawar alluran riga-kafin COVID-19 na kamfanin Sinopharm daga kasar Sin yayin da wannan kasar ta gabashin Afrika ke kara azama wajen yi wa al’umma mafiya hadarin kamuwa da cutar riga-kafin. Jami’an sun nuna cewa, gudummawar alluran daga kasar Sin za su kara karfafa ayyukan yaki da annobar a Kenya.

Susan Mochache, babbar sakatariya a ma’aikatar lafiyar kasar Kenya, wacce take daya daga cikin manyan jami’an gwamnatin kasar da suka yi maraba da isowar alluran riga-kafin a filin jirgin saman Nairobi, wanda kasar Sin ta bayar da gudummawarsu ta ce, riga-kafin da suka karba a wannan rana alamu ne dake kara bayyana kyakkyawar dangantakar dake wakana tsakanin kasashen Kenya da Sin, kuma alakar kasashen 2 ta zarce fannin kiwon lafiya kadai, har ma ta kunshi fannin cinikayya da sauran fannonin raya kasa.

Hukumar kula da ingancin magunguna ta kasar Kenya ta riga ta amince da yin amfani da riga-kafin kamfanin Sinopharm na kasar Sin, tare da sauran riga-kafin na kamfanonin Moderna, Johnson&Johnson, Pfizer da AstraZeneca, yayin da kasar ke kara gaggauta yi wa al’ummar kasar riga-kafin.

Madam Mochache ta kara da cewa, zuwan riga-kafin na Sinopharm wani muhimmin mataki ne a kokarin da kasar Kenya ke yi na yaki da annobar da kuma gaggauta farfadowar al’amurra a kasar.

Zhang Yijun, babban jami’in diflomasiyyar ofishin jakadancin kasar Sin a Kenya, ya ce gudummawar riga-kafin da kasar Sin ta samar sun kara tabbatar da muhimmancin huldar dake tsakanin kasashen Sin da Kenya.(Ahmad)

Ahmad