logo

HAUSA

An cika kwana 1,500 na fara amfani da sabon layin dogon da Sin ta gina a Kenya

2021-07-10 16:42:45 CMG

An cika kwana 1,500 na fara amfani da sabon layin dogon da Sin ta gina a Kenya_fororder_kenya

Layin dogo na zamani da Sin ta gina tsakanin birnin Mombasa da Nairobin Kenya, ya cika kwanaki 1,500 da fara aiki ba tare da wata tangarda ba, yayin da yake bunkasa zirga-zirgar kayayyaki da fasinjoji cikin aminci.

Sanawar da kamfanin AfriStar mai kula da ayyukan jirgin ya fitar jiya a Nairobi, ta ce hidimar jirgin kasan na zamani, na kan gaba cikin sauye-sauyen zaman takewa da tattalin arziki na kasar cikin shekaru 4 da suka gabata, wato bayan ya fara aiki.

A cewar sanarwar, sufurin jirgin da ma karuwar muhimmancinsa ga harkokin al’umma ya kara masa karbuwa a tsakanin jama’a da masu jigilar kayayyaki.

Kamfanin AfriStar ya ce cika kwanaki 1,500 da fara aiki, alama ce ta ci gaban da aka samu na gudanar ayyukansa cikin aminci da inganci da nagarta, kuma jama’ar Kenya da Sinawa da gwamnatocin yankuna ma, sun jinjinawa ayyukan jirgin.

Ya kara da cewa, jirgin na bunkasa yakin da Kenya ke yi da COVID-19 ta hanyar tabbatar da jigilar muhimman kayayyakin ba tare da tsaiko ba. (Fa’iza Mustapha)

Fa'iza