logo

HAUSA

FAO na neman dala miliyan 130 domin tallafawa yankin gabashin Afrika dake fama da fari

2022-02-12 17:03:06 CRI

Hukumar samar da abinci da raya aikin gona ta MDD (FAO), ta bayyana bukatar tallafin dalar Amurka miliyan 130, domin taimakawa al’ummomi masu tsananin rauni, a yankunan kasashen Habasha da Kenya da Somalia, dake fama da fari.

Hukumar ta yi gargadin cewa, farin da ake ci gaba da fuskanta na ingiza karancin abinci a yankin kahon Afrika, inda mutane miliyan 12 zuwa 14 ke fuskantar barazana, yayin da tsirrai ke mutuwar dabbobi kuma ke kara rasa kuzari.

Shugaban hukumar a yankin gabashin Afrika, David Phiri, ya ce ana bukatar kara daukar matakai a yanzu, domin kaucewa shiga matsalar jin kai. (Fa’iza Mustapha)

Fa’iza Mustapha