logo

HAUSA

Tawagar hadin gwiwar ECOWAS da MDD ta ziyarci Burkina Faso da ganawa da shugabannin soji

2022-02-01 19:16:32 CMG

Tawagar hadin gwiwar ECOWAS da MDD ta ziyarci Burkina Faso da ganawa da shugabannin soji_fororder_0201-Burkina-Ahmad~1

A ranar Litinin, tawagar hadin gwiwar kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afrika ta yamma (ECOWAS) da MDD, ta gana da shugabannin mulkin sojojin kasar Burkina Faso.

Shirley Ayorkor Botchwey, ministan harkokin wajen kasar Ghana wanda ya jagoranci wakilan ECOWAS, ya bayyana cewa, shugabannin kasashen Afrika ne suka bukaci tawagar ta ziyarci kasar domin tattaunawa da hukumomi da nufin nazarin yanayin da ake ciki tare da duba yadda makomar kasar Burkina Faso zata kasance.

A lokacin ziyarar zuwa kasar ta Burkina Faso, tawagar ta gudanar da tattaunawa da Laftanal Kanal Paul-Henri Sandaogo Damiba, shugaban kungiyar fafutuka da farfadowar kasar (MPSR), wanda shine ke rike da madafun ikon kasar ta yammacin Afrika.

Botchwey yace, makasudin ziyararsu shine domin duba yadda zasu yi aiki tare da Burkina Faso domin taimakawa kasar game da yadda zata fita daga cikin yanayin da ta tsinci kanta a halin yanzu.

Mambobin tawagar hadin gwiwar sun kuma ziyarci hambararren shugaban kasar, Roch Marc Christian Kabore, wanda yana cikin koshin lafiya, kamar yadda ministan harkokin wajen na Ghana ya bayyana.

Tawagar zata gabatar da rahotonta ga ECOWAS a lokacin taron kolinta wanda za a gudanar a ranar Alhamis a Accra.(Ahmad)

Ahmad