logo

HAUSA

Xi Jinping Ya Aike Da Sakon Taya Murnar Taron Kolin AU Karo Na 35

2022-02-05 21:17:20 CMG

Xi Jinping Ya Aike Da Sakon Taya Murnar Taron Kolin AU Karo Na 35_fororder_0205-Xi-AU-Ahmad

A ranar 5 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon taya murna ga taron kolin shugabannin kungiyar tarayyar Afrika AU karo na 35, inda ya bayyana fatan alheri ga kasashen Afrika da al’ummar nahiyar.

Shugaba Xi Jinping, ya bayyana cewa, a wannan shekarar ne ake cika shekaru 20 da kafuwar kungiyar AU. A cikin shekaru 20 da suka gabata, kungiyar tarayyar Afrika ta samu gagarumin cigaba ta hanyar hadin kai da kuma bijiro da hanyoyin mafiya dacewa don samun bunkasuwar Afrika, lamarin da ya haifar da babban tasirin da nahiyar ke dashi a harkokin kasa da kasa da kuma samun matsayin kara cigaba da bunkasuwar Afrika.

Bangaren kasar Sin a shirye take tayi aiki da bangaren Afrika domin jagorantar cigaban hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afrika zuwa sabon matsayi mafi inganci, da fadada cigaban huldarsu, da kuma cigaba da bude sabon shafi na kyautata hadin gwiwar Sin da Afrika.(Ahmad)

Ahmad