logo

HAUSA

UNECA na hasashen yarjejeniyar AfCFTA za ta bunkasa bangaren sufuri a nahiyar Afrika

2022-02-12 16:45:08 CRI

Hukumar kula da tattalin arzikin nahiyar Afrika ta MDD (UNECA), ta ce ana sa ran yarjejeniyar yankin ciniki cikin ‘yanci ta nahiyar Afrika AfCFTA, za ta kara cinikin hidimomin sufuri tsakanin kasashen nahiyar da kusan kaso 50.

Hukumar ta bayyana cikin wata sanarwa a jiya cewa, bangaren sufuri na nahiyar zai matukar amfana daga yarjejeniyar, tana mai cewa, kiyasin da aka yi a baya-bayan nan mai taken “tasirin yarjejeniyar yankin ciniki cikin ‘yanci ta nahiyar kan bukatar sufuri da ababen more rayuwa”, ya nuna cewa, sama da kaso 25 na ribar hidimomin da za a samu daga cinikayya tsakanin kasashen, zai tafi ne ga bangaren sufuri kadai, kuma kusan kaso 40 na karuwar hidimomin a nahiyar zai tafi ga bangaren.

Ta ce nazarin da masana na bangaren makamashi da ababen more rayuwa da hidimomi na hukumar suka yi, ya bayyana damarmakin zuba jari a bangaren na sufuri.

A cewar nazarin, zuwa shekarar 2030, yarjejeniyar za ta bukaci manyan motocin dakon kayayyaki 1,844,000 da manyan motocin dakon kwantainoni 248,000. Idan kuma aka aiwatar da ayyukkan ababen more rayuwa da aka tsara, adadin manyan motocin dakon kayayyaki zai karu zuwa 1,945,000, yayin da na dakon kwantainoni zai karu zuwa 268,000.

Har ila yau, nazarin ya bayyana cewa, bukatar manyan motocin da za su tallafawa yarjejeniyar wajen jigilar kayayyaki a yankin yammacin Afrika kadai ya kai kaso 39, wadanda za su yi jigila daga yammaci zuwa kudancin nahiyar kuma ya kai kaso 19.8, yayin da bukatar motocin daga kudancin nahiyar zuwa yammaci, ya kai kaso 9.9. (Fa’iza Mustapha)

Fa’iza Mustapha