logo

HAUSA

Habasha Ta Samu Kudin Shigar Da Ya Kai Dala Miliyan 104 Daga Yankunan Masana’antun Da Sin Ta Gina

2022-02-12 16:17:29 CRI

Habasha ta samu kudin shigar da ya kai dalar Amurka miliyan 104, daga fitar da kayayyakin da aka samar a yankunan masana’antu da Sin ta gina a kasar.

Daraktan yada labarai na yankin masana’antun na Habasha Henok Asrat, ya ce an samu kudin ne daga kayayyakin da aka fitar cikin watanni 6 na farkon shekarar kudin kasar da ake ciki ta 2021/2022, wadda ta fara daga ranar 8 ga watan Yuli.

Henok Asrat ya kara da cewa, aikin ginin yankin masana’antu na Semera dake gabashin kasar, da kamfanin kasar Sin na CCCC ke gudanarwa, ya kai kaso 97 na kammaluwa.

Ya ce Habasha na da burin ginawa da kaddamar da yankunan masana’antu sama da 30 a fadin kasar, zuwa shekarar 2025, domin cimma burinta na zama cibiyar sarrafa kayayyaki ta zamani.

A cewarsa, gwamnatin Habasha na ba da muhimmanci ga hadin gwiwa da kamfanonin kasar Sin a fannoni daban-daban.

Wannan a cewarsa, ya shafi gina yankunan masana’antu da jarin da manyan kamfanonin kasar Sin suka zuba a cibiyoyin masana’antu daban-daban, wadanda aka gina galibinsu bisa mizani da kuma kudin daga kasar ta Sin. (Fa’iza Mustapha)

Fa’iza Mustapha