logo

HAUSA

Gwamnatin Habasha ta zargi dakarun TPLF da hallaka sama da mutane 100 a Kombolcha dake arewacin kasar

2021-11-02 11:14:43 CMG

Gwamnatin Habasha ta zargi dakarun TPLF da hallaka sama da mutane 100 a Kombolcha dake arewacin kasar_fororder_1102-saminu-5

Gwamnatin kasar Habasha, ta zargi dakarun ‘yan aware na TPLF da hallaka sama da mutane 100, a garin Kombolcha na yankin Amhara dake arewacin kasar, mai iyaka da yankin Tigray dake fama da tashe tashen hankula.

Wani jami’in gwamnatin Habashan ya yi kira ga sassan kasa da kasa, da kada su kawar da kai daga wannan mummunar ta’asa da ‘yan tawayen suka aikata.

Da yake karin haske kan lamarin, kakakin gwamnatin Habasha Legesse Tulu, ya ce ‘yan awaren TPLF sun bi dare, tare da fadawa matasan garin Kombolcha. Wani gari mai kunshe da muhimman masana’antu a yankin Amhara.

Tuni majalissar wakilan kasar Habasha, ta ayyana kungiyar TPLF a matsayin ta ‘yan ta’adda.  (Saminu)

Saminu