Habasha ta sanar da kafa dokar ta baci a duk fadin kasar
2021-11-03 14:16:32 CMG
Gwamnatin kasar Habasha ta sanar da kafa dokar ta baci a duk fadin kasar yayin da tashin hankali ke kara ta’azzara a shiyyar arewacin kasar.
Majalisar ministocin kasar Habasha ce ta amince da daukar matakin, wanda ake sa ran majalisar wakilai ta tarayyar kasar Habasha zata amince da kudirin cikin kwanaki biyu masu zuwa.
Dokar za ta cigaba da aiki har na tsawon watanni shida.(Ahmad)