logo

HAUSA

MDD: Barkewar fada a yankin Afar na kasar Habasha ya haifar da cikas ga ayyukan jinkai a yankin Tigray

2022-02-05 17:04:24 CMG

MDD: Barkewar fada a yankin Afar na kasar Habasha ya haifar da cikas ga ayyukan jinkai a yankin Tigray_fororder_0205-Habasha-Ahmad

Ofishin kula da ayyukan jinkai na MDD, OCHA ya sanar cewa, fadan da ya barke a shiyyar Afar dake arewacin kasar Habasha yayi sanadiyyar karuwar masu bukatar tallafin jinkai, kana ya haifar da koma baya ga ayyukan jigilar kayayyakin agaji zuwa yankin Tigray mai makwabtaka.

OCHA ya jiyo hukumomin shiyyar na bayyana cewa, sama da mutane 200,000 rikicin ya tilastawa ficewa daga gidajensu a sakamakon fada na baya bayan nan da ya barke a shiyyar Afar. Fadan ya kuma hana MDD da abokan huldarta samun damar gudanar da bincike game da girman hasarar da aka samu a yankin. To sai dai, ofishin yace, yayi amanna mutanen da suka kauracewa muhallan nasu suna cikin tsananin bukatar tallafin gaggawa.

A wasu daga cikin yankunan Afar da ake iya samun damar shiga, an samu nasarar kai daukin ga mutane sama da 40,000 inda aka basu taimakon abinci a makon da ya gabata, haka kuma an samar da taimakon ga mutane sama da 420,000 tun daga tsakiyar watan Oktoba, inji ofishin OCHA.

A cewar ofishin agajin, har yanzu an dakatar da ayyukan jigilar kayayyakin agaji zuwa yankin Tigray ta hanyar motar Semera zuwa Abala zuwa Mekelle, sakamakon matsalar tabarbarewar tsaro a yankin Afar. MDD da abokan hulda ko dai sun dena ko kuma sun yi matukar rage ayyukansu sakamakon karancin kayayyaki da man fetur.

A makon da ya gabata, kayayyakin tallafin da aka ragesu an yi hakan ne domin taimakawa mutanen da suka kauracewa gidajensu da kuma alummar dake karbar bakuncinsu a garin Shire. Kididdigar baya baya nan da shirin samar da abinci na MDD ya fitar a makon jiya ta nuna cewa, sama da kashi 80 bisa 100 na mutanen da aka bincika a yankunan suna fama da matsalar rashin abinci, yayin da kusan kashi 40 bisa 100 na mutanen suna cikin yanayin tsananin karancin abinci.(Ahmad)

Ahmad