logo

HAUSA

Gwamnatin Habasha ta jinjinawa nasarar taron FOCAC

2021-12-15 14:10:22 CMG

Gwamnatin Habasha ta jinjinawa nasarar taron FOCAC_fororder_211215-S3Habasha

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Habasha Dina Mufti, ya jinjinawa nasarar da aka cimma, a yayin taron dandalin hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka karo na 8, wanda ya gudana a kasar Senegal cikin watan Nuwamba.

Dina Mufti, wanda ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da ofishin sa ya saba gudanarwa, ya ce taron na FOCAC, ya kara taimakawa wajen karfafa alakar Sin da kasashen nahiyar Afirka.

Dina Mufti, ya ce Habasha na iya amfana daga manyan nasarorin da aka cimma a yayin taron, ciki har da manufar nan ta bude yankin musamman na fitar da albarkatun gonan Afirka zuwa kasar Sin, da shirin samar da kudaden fitar da hajoji daga nahiyar Afirka.

Jami’in ya kuma jaddada imanin sa ga aniyar kasar Sin, ta wanzar da goyon bayan ta ga kasar Habasha dake gabashin Afirka.  (Saminu)

Saminu