logo

HAUSA

Mambobin AfCFTA Sun Kammala Tattaunawa Kan Wasu Ka’idoji

2022-01-30 17:03:09 CRI

Kasashe mambobin yarjejeniyar ciniki maras shinge na nahiyar Afrika (AfCFTA), a ranar Asabar, sun kammala tattaunawa kan ka’idojin wuraren samar da kaya na asali, a matsayin wani kokarin da ake sa ran zai kara rage yawan kudin harajin kayayyakin da ake samarwa a cikin nahiyar Afrika.

Ebrahim Patel, shugaban majalisar ministocin kasuwanci a kungiyar tarayyar Afrika AU, ya fadawa manema labarai cewa, ka’idojin za su shafi kashi 87.7 bisa 100 na kayayyakin da ake samarwa a tsakanin kasashe mambobin AU.

“Wannan muhimmin ci gaba ne a tarihi," a cewar Patel, ya kara da cewa, ka’idojin wuraren samar da kaya na asali da aka amince da su za su kasance a matsayin wani tushe na samun cikakkiyar hada-hadar kasuwanci a tsakanin kasashe mambobin dake karkashin yarjejeniyar ciniki maras shinge ta Afrika, domin samun nasarar bunkasuwar tattalin arzikin Afrika.

Ya ci gaba da cewa, ga al’umma ‘yan asalin nahiyar, hakan na nufin za a samu karin guraben ayyukan yi, da karin damammakin tattalin arziki, kana wata babbar dama ce ga nahiyar Afrika ta samun bunkasuwar masana’antu. Bai kamata a ce nahiyar aikinta kadai shi ne samar da kayayyakin da masana’antu ke sarrafawa ba.

Wamkele Mene, babban sakataren AfCFTA, ya yi nuni da cewa, kammala tattaunawa kan ka’idojin wuraren samar da kaya na asali, wani muhimmin ci gaba ne wajen cimma nasarar aiwatar da yarjejeniyar cinikayya maras shinge ta nahiyar.(Ahmad)

Ahmad