logo

HAUSA

Zhao Lijian: Sin na fatan sassan kasa da kasa za su yi hadin gwiwa wajen taimakawa tsibiran dake tekun Fasifik

2022-02-11 19:58:02 CRI

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya ce Sin na fatan dukkanin kasashen duniya za su yi hadin gwiwa, wajen aiwatar da matakan taimakawa tsibiran dake tekun fasifik, ta yadda za su shawo kan kalubalolin su. Kaza lika sassan kasa da kasa za su ingiza manufofin wanzar da zaman lafiya, da daidaito, da ci gaba a yankin tsibiran.

Rahotanni na cewa, a gobe Asabar, sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, zai isa Fiji domin gudanar da ziyara. Kuma a yayin da alakar Sin da kasashen tsibiran fasifik ke kara karko, Amurka na son amfani da ziyarar ta Mr. Blinken, wajen dakushe tasirin Sin a yankin. Game da wannan batu, Zhao Lijian ya bayyana cewa, bunkasa ci gaban dangantakar Sin da tsibiran fasifik abu ne a bayyane, wanda ake yin sa a fili, ya kuma hade dukkanin sassa, kuma ba shi da manufar muzgunawa wani bangare na daban.

Zhao ya kara da cewa, yayin da Sin ke gina kyakkyawar alaka da tsibiran na tekun fasifik, tana kuma martaba ka’idojin wanzar da daidaito tsakanin dukkanin kasashe manya da kanana, tana girmama adalci, da burin cimma moriyar juna, da rike gaskiya, da kokarin cimma sakamako, bisa zaman karko da amincewa juna.

Jami’in ya ce, Sin a shirye take ta tallafawa manufar kafa al’ummar bil Adama mai makomar bai daya, tsakanin ta da tsibiran na tekun fasifik, matakin da tuni ya samu karbuwa matuka daga gwamnatoci, da al’ummun kasashen baki daya.   (Saminu)

Saminu