logo

HAUSA

Sin ta bukaci Amurka da ta kawar da karin haraji da takunkumai da ta kakaba mata

2022-02-10 20:48:07 CRI

Kakakin ma’aikatar kasuwancin kasar Sin Gao Feng, ya ce Sin na fatan Amurka za ta gaggauta soke karin haraji, da takunkumai, da ma sauran matakai da take dauka na muzgunawa Sin.

Gao Feng, wanda ya bayyana hakan a yau Alhamis, yayin taron manema labarai da ya gudana, ya ce Sin na aiki tukuru don aiwatar da yarjejeniyar tattalin arziki da cinikayya tsakanin ta da Amurka a mataki na farko, tun lokacin da aka amince da aiwatar da hakan. Kaza lika Sin tana kuma kokarin ganin an shawo kan tarin matsaloli masu nasaba da annobar COVID-19, da koma bayan tattalin arziki, da katsewar tsarin samar da hajoji.

Jami’in ya kuma yi kira ga Amurka, da ta samar da kyakkyawan yanayi, da tsare tsare, da za su taimakawa sassan biyu wajen fadada hadin gwiwar cinikayya.  (Saminu)

Saminu