logo

HAUSA

Sin: Ya dace duk wata cudanya ta kasa da kasa ta dace da zamani

2022-02-09 20:14:21 CRI

Sin: Ya dace duk wata cudanya ta kasa da kasa ta dace da zamani_fororder_赵立坚

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya ce kamata ya yi duk wata cudanya tsakanin sassan kasa da kasa, ta dace da zamanin da ake ciki, wato wanzar da zaman lafiya da ci gaba, kana ta haifar da kyakkyawan yanayin amincewa da juna, da hadin kan kasa da kasa.

Zhao Lijian, ya yi wannan tsokaci ne yayin taron manema labarai na Larabar nan, gabanin taron ministocin harkokin waje na kasashen Amurka, da Australia, da Japan da India, wanda zai gudana a Australia.

Tuni dai sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya isa Australia a yau, domin halartar taron. Kafin hakan, mataimakin sa mai lura da harkokin yankin gabashin Asiya da fasifik Daniel Kritenbrink, ya bayyana a Juma’ar makon jiya, cewa taron dake tafe, zai ba da damar shawo kan abun da ya kira “Kalubalen da Sin ke haifarwa” ga dimokaradiyya, da tsarin gudanar da harkokin kasa da kasa.

Game da hakan, Zhao ya ce dimokaradiyya mallakin daukacin bil Adama ce, ba wai ta wata kasa ko wasu tsirarun kasashe ba. Don haka al’ummun kasa ne ke da ikon fayyace ko kasar su na bin salon dimokaradiyya ko a’a.

Jami’in ya kuma soki lamirin Amurka, bisa yunkurin ta na cusawa sauran kasashen duniya mizanin ta na dimokaradiyya, tare da hada wasu rukunoni da ta amince su ne ke bin tsarin dimokaradiyya, matakin da a cewar Zhao, keta hurumin dimokaradiyya ne.

Daga nan sai ya kara da cewa, kasar Sin da mafi yawan kasashen duniya sun gamsu, suna kuma bin tsarin gudanar da harkokin kasa da kasa bisa tushen MDD, da sauran dokokin cudanyar kasashen duniya, maimakon biyewa dokokin da wata kasa guda ke kafawa sauran kasashe.  (Saminu)

Saminu