logo

HAUSA

Sin da Amurka za su gudanar da jerin ayyuka na tunawa da ziyarar da tsohon shugaban Amurka Richard Nixon ya gudanar a Sin

2022-02-10 19:59:23 CRI

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya ce Sin da Amurka za su gudanar da wasu jerin ayyuka, na bikin cika shekaru 50 da ziyarar da tsohon shugaban Amurka Richard Nixon ya gudanar a Sin, inda ya kuma sanya hannu kan sanarwar Shanghai.

Zhao wanda ya bayyana hakan a yau Alhamis, ya ce sanarwar Shanghai, ita ce irin ta ta farko da kasashen biyu suka sanya hannu, wadda ta kafa wasu ka’idoji da sassan biyu za su bi, domin bunkasa kawancen su, musamman tabbatar da manufar “kasar Sin daya tak a duniya”, wadda ta zama ginshikin daidaita alakar sassan biyu, da kuma kafa huldar diflomasiyya tsakanin su.    (Saminu)

Saminu