logo

HAUSA

Rundunar sojojin kasar Sin ta sha alwashin dakile duk wani yunkuri na tsoma hannun sassan waje cikin harkokin cikin gidan kasar

2022-02-09 20:26:35 CRI

Rundunar sojojin kasar Sin ta sha alwashin dakile duk wani yunkuri na tsoma hannun sassan waje cikin harkokin cikin gidan kasar_fororder_中美2

Kakakin ma’aikatar tsaron kasar Sin Wu Qian, ya ce rundunar sojojin kasar za ta yi duk mai yiwuwa, wajen dakile duk wani yunkuri na tsoma hannun sassan waje, cikin harkokin cikin gidan kasar, da duk wani yunkuri na masu burin ballewar yankin Taiwan, kaza lika za ta kara kaimi wajen tabbatar da dinkewar sassan kasar Sin.

Wu Qian, wanda ya yi wannan tsokaci a Larabar nan, yayin da yake amsa tambaya game da shirin gwamnatin Amurka, na sayarwa yankin Taiwan makamai, ya ce matakin Amurkan ya yi matukar sabawa manufar nan ta “kasar Sin daya tak a duniya”, da sanarwar hadin gwiwa guda 3 da Sin da Amurkan suka amince, musamman ma wadda aka fitar bayan taron sassan biyu na ranar 17 ga watan Agusta na shekarar 1982.

Wu ya kara da cewa, Amurka ta aiwatar da matakai na tsoma hannu cikin harkokin cikin gidan Sin, ta kuma illata manufar kasar Sin game da mulkin kai da tabbatar da tsaro, kana ta haifar da koma baya, ga hadin gwiwar sassan biyu a fannin ayyukan soji, baya ga jefa zirin Taiwan cikin yanayi na dar dar, ta fuskar zaman lafiya da daidaito.

Jami’in ya ce Sin na fatan Amurka, za ta gaggauta soke shirin ta na sayarwa Taiwan makamai, da dakatar da duk wasu kwangiloli masu nasaba da ayyukan soji da Taiwan, ta kuma dakatar da nuna tana tare da masu burin ballewar yankin na Taiwan. (Saminu)

Saminu