logo

HAUSA

Zhao Lijian: Sin ta nunawa duniya kyawun manufar wasannin Olympics

2022-02-08 20:14:09 CRI

Wani bidiyo, wanda ya nuna yadda ‘yar wasan kasar Amurka Tessa Maud, ke zubar da hawaye, na shaukin ganin yadda masu aikin sa kai suka fitar da zayyana, mai dauke da jimlar "Maraba da zuwa Sin", lokacin bikin kaddamar da gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi dake gudana yanzu haka a birnin Beijing, ya karade sassan kafofin yanar gizo.

Game da hakan, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana yayin taron manema labarai na Talatar nan cewa, tun lokacin bude wannan gasa ta lokacin hunturu da birnin Beijing ke karbar bakunci, an samu labaran wasu abubuwa masu motsa zukata da suka faru, wadanda ke nuni ga yanayi na abota da goyon bayan juna.

Zhao ya ce, da yawa daga ‘yan wasan dake halartar gasar, sun bayyana gamsuwa, da jinjinawa dukkanin tsare tsare da suka gani a kasar Sin, sun kuma bayyana yadda suke farin ciki a kullum, idan sun hadu da masu aikin sa kai cike da murmushi suna daga musu hannu.

Zhao Lijian ya kara da cewa, kusan ‘yan wasa 3,000 daga kasashen duniya da yankuna 91 ne suka taru, a wannan birnin mai tarihin karbar bakuncin gasannin Olympics guda biyu, inda suke fafatawa a karkashin tutar wannan gasa, suna farin ciki da jin dadin yanayin da gasar ke tattare da shi.

‘Yan wasa daga sassan duniya daban daban, baya ga taken gasar da suke nunawa, na "Sauri, da kara dagawa, da karfi, a hannu guda suna cike da hadin kai a lokacin gudanar da gasar, sun kuma kawar da duk wasu shingaye, tare da karfafa kawance, da musaya, da cudanya a gefen fafatawar da suke yi. Zhao ya ce wannan shi ne kyawun manufar wasannin Olympics.    (Saminu)

Saminu