logo

HAUSA

Kwamitin tsaron MDD ya bukaci a gaggauta sakin shugaban Burkina Faso

2022-02-10 20:18:28 CRI

Kwamitin tsaron MDD, ya bukaci sojoji da su gaggauta sakin shugaban kasar Burkina Faso Roch Marc Christian Kabore, da sauran jami’an gwamnatin sa dake tsare.

Wata sanarwar da kwamitin tsaron ya fitar a jiya Laraba, ta bayyana damuwar kwamitin, game da sauyin gwamnati wanda ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar. Sanarwar ta kara da cewa, mambobin kwamitin sun lura da matakin da kungiyoyin ECOWAS da AU suka dauka, na dakatar da Burkina Faso daga cikin su, har sai sojojin kasar masu juyin mulki sun amince da komawa tanadin kundin tsarin mulkin kasar.

Kaza lika, kwamitin tsaron ya ce yana goyon bayan matakin shiga tsakani da sassan shiyyar ke yi, domin kawo karshen takaddamar siyasa a Burkina Faso. Mambobin kwamitin sun kuma nuna damuwa, game da illar dake tattare da yawaitar juyin mulki ba bisa ka’ida ba a yankin yammacin Afirka, da bunkasar ayyukan kungiyoyin ta’addanci, da ma mummunan tasirin su ga zamantakewa da tattalin arzikin al’ummun yankin. (Saminu)

Saminu