ECOWAS ta dakatar da Burkina Faso daga zama mambarta
2022-01-29 17:03:57 CRI
Kungiyar raya tattalin arzikin yammacin Afrika ECOWAS, ta sanar da dakatar da Burkina Faso daga matsayinta na mamba, saboda juyin mulkin sojoji a kasar.
An dauki wannan mataki ne biyo bayan taron shugabannin kasashen yankin da aka yi ta kafar bidiyo a jiya Juma’a.
A ranar Litinin ne, rundunar sojin Burkina Faso ta sanar ta kafar talabijin cewa, sojoji sun kwace mulki tare da kawo karshen ayyukan shugaban kasar Roch Marc Christian Kabore.
Sanarwar bayan taron shugabannin ECOWAS ta ruwaito cewa, sojojin sun tilastawa shugaba Kabore yin murabus, inda suka nemi sojojin su sake shi, tare da sauran ‘yan siyasar dake tsare.
A cewar sanarwar, za a tura tawagogin kungiyar biyu karkashin kwamitin manyan hafsoshinta da majalisar ministoci zuwa Burkina Faso, domin tantance yanayin tsaro da siyasar kasar.
Bugu da kari, shugabannin na kasashen ECOWAS, za su kara haduwa a Accra babban birnin Ghana a ranar Alhamis, domin sake nazarin yanayin kasashen Burkina Faso da Guinea da Mali. (Fa’iza Mustapha)