logo

HAUSA

ECOWAS za ta shirya taron koli kan yanayin da ake ciki a Burkina Faso

2022-01-26 10:51:54 CRI

ECOWAS za ta shirya taron koli kan yanayin da ake ciki a Burkina Faso_fororder_220126-A2-ECOWAS

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afrika ta yamma (ECOWAS), ta bayyana a wata sanarwa a jiya Talata cewa, biyo bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a Burkina Faso, za ta kira babban taro nan da wasu kwanaki masu zuwa domin yin nazari game da halin da ake ciki a kasar.

ECOWAS ta kuma yi Allah wadai da babbar murya bisa juyin mulkin sojojin, wanda ta bayyana a matsayin babban koma baya ga tsarin mulkin demokaradiyyar kasar Burkina Faso.

A cewar sanarwar, ba zai taba yiwuwa a warware matsalolin kasar ta hanyar soji ba, tattaunawa da yin maslaha, su ne kadai hanyoyin da za su magance tashin hankali da kuma samun zaman lafiya mai dorewa a kasar. (Ahmad Fagam)