logo

HAUSA

Kamaru da Burkina Faso sun kai zagayen kusa da karshe a gasar AFCON

2022-01-30 17:07:34 CRI

Jamhuriyar Kamaru mai masaukin baki da kasar Burkina Faso, sun tsallaka zuwa matakin zagayen kusa da karshe a gasar wasan kwallon kafa ta cin kofin kasashen Afrika (AFCON) dake gudana a halin yanzu.

A wasan da suka buga na zagayen kusa da na kusan karshe da yammacin ranar Asabar, a filin wasa na Japoma dake birnin Douala, Kamaru ta yi nasara bayan ta lallasa kasar Gambia da ci 2 da 0.

Kamaru wacce ta taba lashe kofin sau biyar, za ta kara a wasan zagayen karshe da kasar da za ta yi nasara tsakanin kasashen Masar da Morocco a zagaye na gaba wanda za a buga a ranar Lahadi.

Kazalika, a daren ranar Asabar an yi waje da kasar Tunisia a gasar ta AFCON, bayan wasansu da Burkina Faso inda aka tashi da ci 1-0 a filin wasan Roumde Adjia dake birnin Garoua (North).

A wasan kusa da karshe, Burkina Faso za ta kara ne ko dai da kasar Equatorial Guinea, ko kuma kasar Senegal wanda ake sa ran za su fafata wasansu na kusa da kusan karshe a ranar Lahadi.(Ahmad)

Ahmad