logo

HAUSA

Sin ta bukaci Amurka da ta kawar da yiwuwar sayarwa Taiwan da makamai

2022-02-08 19:42:02 CRI

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya ce Sin na kira ga Amurka, da ta kawar da yiwuwar sayarwa yankin Taiwan makamai, duba da cewa yin hakan, zai yi matukar keta hurumin manufar “kasar Sin daya tak a duniya”.

Zhao Lijian ya bayyana hakan ne, a yayin taron manema labarai da ya gudana a Talatar nan.   (Saminu)

Saminu