logo

HAUSA

Sin ta yi Allah wadai da kudurin dokar takara da Amurka ta kafa wadda ke cike da salon cacar baka

2022-02-07 19:39:31 CRI

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya soki lamarin dokar takara da Amurka ta kirkira, wadda ke cike da salon cacar baka, da yunkurin bata sunan kasar Sin a idanun duniya, da kushe salon ci gaban kasar ta Sin, da ma manufofin ta na cikin gida da na waje.

Dokar mai lakabin "America COMPETES Act of 2022", wadda majalissar dokokin Amurka ta amince a makon jiya, ta zama tamkar kutse ne cikin harkokin cikin gidan kasar Sin. Kuma a cewar Zhao Lijian, Amurka na da zabi game da yadda za ta bunkasa salon ta na takara, sai dai duk da haka, bai dace ta yi amfani da batun neman ci gaba wajen tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar Sin ba.    (Saminu)

Saminu