logo

HAUSA

Biden ya sanar da sabbin matakai yayin da tashin hankali ya karu a fadin Amurka

2022-02-04 19:49:14 CMG

Biden ya sanar da sabbin matakai yayin da tashin hankali ya karu a fadin Amurka_fororder_0204-Biden-Ibrahim

shugaban kasar Amurka Joe Biden jiya Alhamis, ya sanar da daukar sabbin matakai, da nufin rage tashe-tashen hankula masu nasaba da harbin bindiga a fadin kasar.

Wata sanarwa da fadar White house ta fitar na cewa, gwamnatin Biden za ta kawo kashen kwararar bindigogi a cikin kasar ba bisa ka'ida ba, da taimakawa masu gabatar da kara su gabatar da kararraki kan wadanda ke amfani da bindigogi na bogi, da wadanda ba su da tsari, da wadanda ba za a iya gano su ba, ana aikata laifuka da su, da zakulo masu sayar da bindigogi ba bisa ka'ida ba da sauransu..

A yammacin jiya ne dai, shugaba Biden ya kai ziyara birnin New York, inda ya yi kira da a kara samar da kudade ga jami’an ‘yan sanda da na tsaro.

Sai dai shugaban na Amurka yayin wani taron da aka shirya a hedkwatar 'yan sandan birnin New York da ke Lower Manhattan, ya bayyana cewa, amsar ba ita ce watsi da titunanmu ba. Yana mai cewa, amsar ba ita ce a samarwa 'yan sanda kudi ba, amsar ita ce a samar musu da kayan aiki, da horo, da kudade don zama abokan hulda, ta yadda za su kasance masu samar da tsaro.

Bayanai na nuna cewa, a wannan shekara kadai, an kashe mutane 1,554 a tashe-tashen hankula a Amurka.(Ibrahim)

Ibrahim