logo

HAUSA

Yawan Amurkawan da COVID-19 ta kashe ya zarce 900,000

2022-02-05 17:02:55 CMG

Yawan Amurkawan da COVID-19 ta kashe ya zarce 900,000_fororder_0205-US-Ahmad

Kasar Amurka ta kafa tarihi mai muni yayin da adadin Amurkawan da suka mutu a sanadiyyar annobar COVID-19 ya zarce 900,000 ya zuwa ranar Juma’a, kamar yadda alkaluman da jami’ar Johns Hopkins ta fitar suka nuna.

Yayin da adadin mutanen da suka kamu da cutar ya kai miliyan 76.2,  jimillar mutanen da suka mutu a kasar ya kai 900,528 ya zuwa karfe 5:22 na yammaci agogon kasar, daidai da karfe 22:22 agogon GMT.

Jahar California ne ke kan gaba a yawan mutanen da cutar COVID-19 ta kashe, inda take da yawan mamata 80,798. Texas ita ne jaha ta biyu mafi yawan mutanen da suka mutu a sanadiyyar cutar inda take da mutane 80,459, sai Florida ke bi mata baya da mutane 65,993 da suka rasu, sai kuma jahar New York inda cutar ta hallaka mutane 65,578, kamar yadda alkaluman suka nuna.

Jahohin dake da adadin wadanda suka mutu da suka zarce 30,000 sun hada da Pennsylvania, Ohio, Illinois, Georgia, Michigan da New Jersey.

Amurka ta kasance kasar dake kan gaba a duniya da cutar COVID-19 tafi yiwa mummunar illa, inda take da adadi mafi yawa na mutanen da suka mutu da kuma mutanen da suka kamu da cutar a duk duniya, a bisa ga alkaluman, kasar tana da kusan kashi 20 bisa 100 na yawan masu kamuwa da cutar sannan tana da kashi 15 bisa 100 na adadin mutanen da suka mutu a sanadiyyar cutar na duk duniya.(Ahmad)

Ahmad