logo

HAUSA

Sakataren MDD ya nuna damuwa kan yadda fararen hula suka mutu a harin da Amurka ta kai wa shugaban IS

2022-02-04 19:46:24 CMG

Sakataren MDD ya nuna damuwa kan yadda fararen hula suka mutu a harin da Amurka ta kai wa shugaban IS_fororder_0204-UN-IS-Ibrahim

Babban sakataren MDD Antonio Guterres, jiya Alhamis ya bayyana damuwarsa kan yadda fararen hula suka rasa rayukansu a harin da Amurka ta kai, wanda ya yi sanadin mutuwar shugaban kungiyar IS Abu Ibrahim al-Hashimi al-Qurayshi.

Da aka nemi jin ta bakin babban sakataren game da harin da Amurka ta kai Syria kan al-Qurayshi, Farhan Haq mataimakin kakakin Guterres ya ce, mun lura da sanarwar da shugaban Amurka Joe Biden ya fitar game da mutuwar Abu Ibrahim al-Qurayshi,shugaban kungiyar ta Da'esh ko IS, mun kuma damu da rahotannin da ke cewa, an kashe fararen hula.

Haq ya ce, muna ci gaba da yin kira ga dukkan bangarori, da su dauki dukkan matakan da suka dace, don kare fararen hula da kayayyakin more rayuwa, bisa la'akari da wajibcin da suka rataya a wuyansu a karkashin dokokin jin kai.

Yana mai cewa, yana da muhimmanci a gudanar da bincike, a kokarin tantance wadanda dake da hannu na mutuwar mutanen a harin.(Ibrahim)

Faeza