logo

HAUSA

Zhao Lijian: Bai dace a yi amfani da mizani biyu a yaki da ta’addanci ba

2022-02-08 19:53:15 CRI

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya ce Sin na lura matuka da halin da ake ciki, game da sanawar da Amurka ta fitar, don gane da kisan shugaban kungiyar IS Abu Ibrahim al-Hashimi al-Qurayshi.

Zhao ya amince cewa, ta’addanci abokin gabar dukkanin kasashen duniya ne, kuma Sin ta sha nanata adawar ta da duk wani nau’in ayyukan ta’addanci a matakin kasa da kasa. A lokaci guda kuma, Sin ba ta yarda da amfani da mizani 2 a yaki da ta’addanci ba, tana mai fatan za a kawo karshen dukkanin wani yanayi na ta’addanci a duniya.    (Saminu)

Saminu