logo

HAUSA

Kasar Sin ta samu lambar yabo ta zinare ta farko a wasannin Olympics

2022-02-06 17:26:52 CMG

Kasar Sin ta samu lambar yabo ta zinare ta farko a wasannin Olympics_fororder_0206-Skating-Faeza

Kasar Sin ta samu lambar zinare na farko a wasanta na zamiyar kankara na gajeren zango a wasannin Olympics dake gudana a birnin Beijing na kasar.

‘Yan wasan kasar Sin 4 da suka hada da Fan Kexin da Qu Chunyu da Ren Ziwei da Wu Dajing ne suka samu nasarar a wasan na mita 2,000 yayin gasar Olympics na hunturu dake gudana, cikin sa’a 2: 37.348, inda suka doke Italiya da ta kammala a sa’a 2:37.364.

Kasar Hungary ce kuma ta samu lambar tagulla a sa’a 2:40.900

Bayan kammala wasan, cikin hawaye, Fan Kexin ta ce ta dade tana jiran wannan lambar Zinare. Tana mai cewa, tana cike da imani kan kungiyarsu da kuma abokan wasanta.

Wannan nasarar, kari ne a kan nasarorin kasar Sin na wasan zamiyar kankara na gajeren zango. Tun daga wasannin Salt Lake City na shekarar 2002, ‘yan wasan kasar Sin ke lashe a kalla lambar zinare 1 a duk wasan da ya biyo baya. (Fa’iza Mustapha)

Faeza